Isa ga babban shafi
Australia

Macron ya karrama tsaffin sojin Australia

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Fira Ministan Australia Malcolm Turnbull yayin gaisawa da tsaffin sojin Australia da iyalansu, a lokacin bikin tunawa da gudunmawar mazan jiya a birnin Sydney.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Fira Ministan Australia Malcolm Turnbull yayin gaisawa da tsaffin sojin Australia da iyalansu, a lokacin bikin tunawa da gudunmawar mazan jiya a birnin Sydney. AAP/David Moir/via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yabawa kasar Australia dangane da rawar da take takawa wajen bada gudumawar sojoji domin shawo kan rikice-rikice a kasashen duniya, ciki har da taimakon da ta bayar a lokacin yakin duniya na farko wajen kawo karshensa.

Talla

Macron yace a madadin Faransa yana mika godiya ta musamman ga Australia, yayin da ya bayyana fatan ganin sun gina dangantaka mai dorewa bayan ginawa kasar jirgin ruwan dake daukar jiragen yaki wanda yanzu haka ke gudana a Faransa.

Shugaban na Faransa ya bayyana haka ne yayinda yake ziyara a kasar ta Australia inda ya gana da Fira Minstan kasar Malcolm Turnbull.

Ganawar shugabannin biyu ta mayar da hankali ne akan yadda zasu shawo kan barazanar mamaye sha’anin kasuwanci, tattalin arziki da kuma uwa uba tasirin Diflomasiyya da kasar China ke samun nasara akai a tsakanin kasashe da tsibirai da yankin yammacin tekun Pacific.

Wata kididdiga da jami’an Australia suka gudanar ta nuna cewa a tsakanin shekarun 2006 zuwa 2016, kasar China, ta baiwa kasashe ko gwamnatocin yankunan da ke yankin na yammacin tekun Pacifi taimakon kudade da yawansu ya kai kusan dala biliyan $2.

Yayin ziyarar ta Macron, wanda shine shugaban Faransa na biyu a tarihi da ya ziyarci Australia, kasashen biyu sun cimma kulla yarjejeniyar karfafa sha’anin tsaro da musayar bayanan sirri, sai kuma kulla alakar ci gaban fasahar samar da makamashi musamman daga hasken rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.