Isa ga babban shafi
Amurka

Weinstein na fuskantar zargin yi wa mata fyade

sanannen Furodusan fina-finai na Nollywood a kasar Amurka Hervey Weinstein yayin fitowa daga hedikwatar 'yan sandan Amurka a birnin New York.
sanannen Furodusan fina-finai na Nollywood a kasar Amurka Hervey Weinstein yayin fitowa daga hedikwatar 'yan sandan Amurka a birnin New York. AFP Photo/Bryan R. Smith

A yau Jumu’a aka gurfanar da wani sanannen Furodusan fina-finai na Nollywood a kasar Amurka wato Hervey Weinstein, bisa zarginsa da aikata fyade da kuma cin zarafi ta hanyar fasikanci.

Talla

To sai dai Harvey ya gabatar da tsabar kudi har Dolar Amurka miliyan 1 domin amsar kansa Beli, watanni 8 bayan da ya rasa kimar aikinsa da ta biyo bayan zarge-zargen aikata lalata.

Wannan badakala da ta mamaye Hervey Weinstein dai ta samo asali ne a ran 5 ga watan Okotoban Bara, inda wata Jarida mai suna New York Times ta ruwaito korafe-korafe daga mata da dama da ke zargin Hervey da keta masu mutunci.

Wata mai haskawa a fina-finan Italiya Asia Argento ta ce Weinstein ya yi mata fyade a shekarar 1997.

Karin wasu shahararrun ‘yan fim din da suka hada da Gwyneth Paltrow, Angelina Jolie and Rosanna Arquette sun zargi Weinstein da cin zarafinsu.

Sai dai wani kakakin Weinstein ya ce sahararren Furodusan ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.