Isa ga babban shafi
Faransa-Isra'ila

Faransa ta bukaci a ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran

Emmanuel Macron da  Benyamin Netanyahu à fadar  l'Elysée, a Faransa
Emmanuel Macron da Benyamin Netanyahu à fadar l'Elysée, a Faransa REUTERS/Philippe Wojazer/Pool

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a ganawar sa da Firaminitan Isra'ila yayi gargadi domin ganin an kaucewa samun tashin hankali sakamakon shirin Iran na cigaba da tace sinadarin uranium domin bunkasa makamashin ta.

Talla

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu wanda ke ziyarar neman goyan bayan kasashen Turai wajen ganin sun yi watsi da yarjejeniyar Iran, bai samu biyan bukata ba daga shugaban Faransa Emmanuel Macron kamar yada shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shaida masa.

Firaminista Netanyahu ya cigaba da zargin Iran a matsayin mai nema jefa gabas ta tsakiya da kuma Turai cikin tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.