Isa ga babban shafi
Faransa

An ceto mutane biyu da wani ya yi garkuwa da su a Paris

Kokarin yan Sanda na ceto mutanen da dan bindiga ke karguwa da su a Faransa
Kokarin yan Sanda na ceto mutanen da dan bindiga ke karguwa da su a Faransa REUTERS/Benoit Tessier

‘Yan sanda a kasar Faransa sun bayyana kama dan bindigar nan da ya yi garkuwa da mutane biyu a tsakiyar birnin Paris, tare da kubutar da mutanen da yake garkuwa da su kuma cikin koshin lafiya, ciki har da wanda aka sama an watsa masa Fetir a jiki.

Talla

An dai fara aikin kama dan bindigar ne da misalin karfe 4 na yamma inda wani gidan Talabijin na cikin gida a kasar ta Faransa ke cewar mutumin ya kutsa kai ne a ofishin wani kamfani da ke a unguwar Rue des Petites Ecuries layi na 10 .

An jikkata mutum daya a lokacin da ake gumurzu da dan bindigar, ya kuma gudu kamin ‘yan sanda su isa a wurin da yake garkuwa da mutanen.

Ba a dai san dalilin dan bindigar na yin garkuwa da mutanen ba, amma dai laifin nashi bai yi kama da na ‘yan ta’adda ba.

Bisa binciken ‘yan sanda dai mutumin na da tabin hankali ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.