Isa ga babban shafi
Wasanni

Gareth Bale zai maye gurbin Ronaldo a Real Madrid

Gareth Bale wanda ke matsayin dan wasa mafi zura kwallaye a Wales, ana ganin abu ne mai kamar wuya ya iya maye gurbin Cristiano Ronaldo wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d'Or har sau 5.
Gareth Bale wanda ke matsayin dan wasa mafi zura kwallaye a Wales, ana ganin abu ne mai kamar wuya ya iya maye gurbin Cristiano Ronaldo wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d'Or har sau 5. Reuters

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Julen Lopetegui ya ce Club din ya shirya tsaf don tunkarar wasannin da ke gabansu a wannan kaka inda dan wasan gaba Gareth Bale zai cike gurbin da Cristiano Ronaldo ya bari.

Talla

Gareth Bale dan Wales mai shekaru 29 wanda a baya shima ya yi yunkurin sauya sheka daga Real din sakamakon abin da ya kira gaza sanya shi a rukunin ‘yan wasan farko da za su rika takawa Club din leda a kowanne wasa yanzu haka zai samu cikakkiyar damar zama zabin farko bayan tafiyar ta Ronaldo.

Da dama dai na zargin tsohon kociyan na Madrid, Zinadine Zidane da fifita Ronaldo akan sauran takwarorinsa na Club din.

A cewar Lopetegui yanzu babu batun sauya shekar Bale, kuma yana farin cikin ci gaba da taka leda a Real Madrid.

Kociyan na Real Madrid ya ce ko Cristiano Ronaldo da ya sauya sheka zuwa Juventus zabi ne daga gare shi amma ba wani sabani ne tsakaninsu da shi ba, kuma sun bar shi ya tafi cikin sauki kasancewar suna da zakakuran 'yan wasan da za su maye gurbinsa.

Bale wanda Lopetuigi ya kira da gwarzon dan wasa ya kulla kwantiragi ne da Madrid a shekarar 2013 kan yuro miliyan 87 inda ya dage kofunan zakarun turai 4 inda ko a wasan karshe na cin kofin zakarun turai sai da ya yi nasarar zura akalla kwallaye 2 cikin 3 da Club din ya ci.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.