Isa ga babban shafi

Maduro ya zargi Colombia da hannu a yunkurin hallaka shi

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, yayin karbar faretin soji a birnin Caracas, a lokacin da bama-bamai suka tarwatse a kusa.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, yayin karbar faretin soji a birnin Caracas, a lokacin da bama-bamai suka tarwatse a kusa. VENEZUELAN GOVERNMENT TV/Handout via REUTERS TV

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya ce yana ci gaba da samun karin kwarin gwiwar aiwatar da manufofin gwamnatinsa fiye da ko yaushe, sa’o’i kalilan bayan yunkurin hallaka shi da aka yi.

Talla

Da fari dai Maduro ya dora alhakin harin bam din da aka kai ta hanyar amfani da wani karamin jirgi mara matuki kan kasar Colombia, amma daga bisani wasu gungun ‘yan tawayen kasar ta Venezuela suka dauki alhakin harin.

Akalla sojin Venezuela bakwai ne suka hallaka a harin da suka kai, yayin da suke tsaka da fareti a Caracas babban birnin kasar.

Shugaba maduro wanda ya bayyana harin a matsayin wani yunkuri na hallaka shi kai tsaye, ya zargi shugaban kasar Colombia mai barin gano, Juan Manuel Santos da hannu wajen kai harin, sai dai nan take ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi watsi da zargin na Maduro.

Sa’o’i kalilan bayan zargin ‘yan adawa da gwamnatin Colombia da da shugaba Maduro ya yi a harin na yau Lahadi, Amurka ta fitar da sanarwa da ke nesanta ta da hannu a yunkurin na hallaka shugaban kasar ta Venezuela.

A cewar mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro, John Bolton, akwai yiwuwar gwamnatin shugaba Maduron ce ta shirya kai harin na karya domin cimma wani buri da ita ce kadai zata iya fayyace shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.