Isa ga babban shafi

Fafaroma Francis ya sha alwashin magance matsalar lalata yara

Pope Francis yayin da ya soma ziyara a kasar Ireland. 25 ga Agusta, 2018.
Pope Francis yayin da ya soma ziyara a kasar Ireland. 25 ga Agusta, 2018. REUTERS/Clodagh Kilcoyne

Fafaroma Francis wanda ke ziyara a kasar Ireland ya bayyana amincewa da gazawar jagorancin mujami’u wajen daukar matakan magance aikata laifukan cin zarafin kananan yara da wasu malaman mujami’u ke yi ta hanyar yi musu fyade.

Talla

Fafaroma Francis wanda ya fara ziyarar tasa a yau Asabar, ya zama jagoran Kiristocin na darikar katolika na farko cikin shekaru 39, da ya ziyarci kasar ta Ireland, tun bayan Fafaroma John Paul na biyu a shekarar 1979.

Fafaroma ya Francis wanda ya gabatar da jawabi ga taron wasu daga cikin mutanen da suka fuskanci cin zarafi a lokacin da suke kananan yara ya ce babu shakka rashin sakacin da aka yi wajen daukar matakan hukunta masu aikata laifukan ya taka rawa wajen yawaitar cin zarafin da bata gari daga cikinsu ke yiwa yara kanana, dabi'ar da ya lashi takobin yakarta.

A yan watanni da suka gabata ne, Fafaroma Francis ya amince da murabus din wasu limaman darikar katolika, da suka hada da na kasar Chile, Austaralia da Amruka, wadanda aka samu da laifin yin lalata da kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.