Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Dubban 'yan Birtaniya na zanga-zangar ficewar kasar daga EU

Dandazon masu zanga-zangar rike da kwalaye na neman lallai majalisar dokokin kasar ta tilasta amincewa a kara kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a gabanin ficewar nan da watanni 5.
Dandazon masu zanga-zangar rike da kwalaye na neman lallai majalisar dokokin kasar ta tilasta amincewa a kara kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a gabanin ficewar nan da watanni 5. REUTERS/Peter Nicholls

Dubban al’ummar Birtaniya masu adawa da shirin ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai ne yau din nan ke gudanar da wata zanga-zangar bukatar sake gudanar da kuri’ar raba gardama kan batun ficewar kasar daga EU.

Talla

Akalla motocin safa-safa 150 ne makare da mutane daga sassa daban daban suka taru a tsakiyar birnin London inda suka fara zanga-zangar tare da neman lallai a sake kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan ficewar a dai dai lokacin da ya rage watanni 5 kacal kasar ta kammala ficewa daga EU.

Dubban masu zanga-zangar za kuma su karkare da tattaki a farfajiyar majalisar dokokin kasar don neman amincewar su kan sake kada kuri’ar.

A ranar 29 ga watan Maris na sabuwar shekara ne Birtaniyar za ta kammala ficewa daga EU ko da dai kawo yanzu ta gaza cimma wata kwakkwarar yarjejeniya haka zalika ta gaza lalubo makomar yankin Arewacin Ireland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.