Isa ga babban shafi
Amurka

Gobarar dajin California ta raba mutane dubu 150 da muhallansu

Wani sashi na jihar California da gobarar daji ta kone gidaje da ababen hawa a garin Paradise.
Wani sashi na jihar California da gobarar daji ta kone gidaje da ababen hawa a garin Paradise. AFP / Josh Edelson

Jami’an agaji a jihar California dake Amurka, sun tabbatar mutuwar mutane 9 a dalilin gobarar dajin da ta rutsa da su, wadda yanzu haka ke ci gaba da bazuwa a garin Paradise dake arewacin jihar.

Talla

Jami’an sun ce gobarar dajin ta kone fadin kasa da ya zarta kadada dubu 70 lamarin da ya tilasta kwashe baki dayan mazauna garin na Paradise 26,000.

A jimlace dai jami’an agaji sun kwashe akalla mutane 150,000 daga wuraren da ake fargabar gobarar dajin za ta afkawa, bayan kone sama da gine-gine 2000, a garin Paradise inda ta soma tashi.

Sama da ‘yan kwana kwana dubu 2,200 ne ke kokarin kashe gobarar, tare da taimakon jirage masu saukar ungulu da kuma manyan tankokin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.