Isa ga babban shafi
Turai

Thailand ta tsare wani dan wasan Bahrein

Firaministan Thailand Prayuth Chan-ocha
Firaministan Thailand Prayuth Chan-ocha REUTERS/Athit Perawongmetha

Gwamnatin Australia a yau lahadi ta umurci gwamnatin Thaillande da ta sako wani tsohon dan wasan kwallon kafa na Bahrein da take tsare da shi tun a ranar 27 ga watan Nuwamba,wanda keda takardar dan gudun hijirar siyasa a kasar.

Talla

Hakeem Alarabi mai shekaru 25 na tsare yanzu haka a kasar Thailand, ya na kuma taka leda a kungiyar Melbourne.

Hukumomin Australia sun bayyana damuwa tareda tabbatar da cewa za su ci gaba da neman gani hukumomin Thailand sun salami wanan dan wasa cikin lokaci.

Hukumomin kasar sa ta asali Bahrein na zargin sa da lalata wani ofishin yan Sanda a shekara ta 2012, kasar sa ta Bahrein ta bukaci gani an tisa keyar sa zuwa gida domin amsa laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.