Isa ga babban shafi
Faransa-Italiya

Bama fatan shiga rikici tsakaninmu da Italiya - Faransa

Tsawon lokaci Italiya na caccakar gwamnatin Faransa amma Faransar taki mayar mata da zazzafan martini.
Tsawon lokaci Italiya na caccakar gwamnatin Faransa amma Faransar taki mayar mata da zazzafan martini. AFP Photos/Ludovic Marin

Gwamnatin Faransa ta mayar da martini kan zargin da Italiya ta yi mata na zamowa sillar kwararowar baki nahiyar Turai dama rashin cancantar shugabanta Emmanuel Macron, inda ta ce ba ta fatan fadawa yakin cacar baka tsakanita da Italiyan, maimakon haka fatan ta su ci gaba da aiki tare don magance matsalolin da kasashensu ke fuskanta a matsayinsu na makota.

Talla

Cikin martinin da minista mai kula da harkokin faransa a tarayyar Turai Nathalie Loiseau ta fitar a yau, ta ce faransar na fatan ci gaba da ganawa, tattaunawa da ma tuntubar juna tsakaninta da Italiya don magance matsalolin da ke addabar su a matsayinsu na makota maimakon tsayawa cacar baka kan wasu batutuwa.

Tsawon watanni kenan dai gwamnatin Italiya ta bakin mataimakin Firaminista Luigi Di Maio na tunzura maso zanga-zangar kasar ta faransa baya ga caccakar gwamnatin Emmanuel Macron amma ba tare da Paris ta mayar da martini ba, inda a wannan karon, firaminista Matteo Salvini da kansa cikin sakon bidiyo da ya wallafa ya ce ta na fata Faransawa za su tseretar da kansu daga ukubar Emmanuel Macron wanda ya ce ko kadan bai cancanci zama shugaban kasa ba.

Ka zalika shima Di Maio cikin kalamansa na jiya bayan bidiyon ranar Litinin ya bukaci kungiyar Tarayyar Turai ta hukunta Faransa da kasashe makamantanta wadanda ke haddasa kwararowar baki nahiyar baya ga tirsasawa Afrikawan da ke kasar komawa kasashensu.

Ko a bara shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya zargi gwamnatin ta Italiya da mayar da shi babban abokin gabarsa tare da fatan kifewar gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.