Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka ta sha alwashin gurgunta shirin Iran na kera makamai

Iran ta sha alwashin ci gaba da kera sabbin makamai masu linzami.
Iran ta sha alwashin ci gaba da kera sabbin makamai masu linzami. Reuters

Amurka ta sha alwashin ci gaba da daukar matakan matsi kan Iran, har sai kasar ta yi watsi da shirinta na kera manyan makamai masu Linzami.

Talla

Alwashin na Amurka ya zo kwana guda bayan da Iran ta sake bayyana wani sabon makami mai linzami da ta kera mai tafiyar tsawon kilomita 1000, bayaga wanda ta yi nasarar gwajinsa a makon da ya gabata, da ke tafiyar nisan kilomita dubu 1 da 300.

Yayin maidawa Amurka martani, maáikatar tsaron Iran ta ce shirinta na kera manya makamai masu linzami na kare kai ne da kuma bunkasa karfin sojinta, dan haka babu wata kafa da kasar za ta bayar ta tattaunawa kan shirin nata, ballatana wata kasa ta nemi ta yi watsi da shi, saboda bukatunta.

A watan Mayu na shekarar bara, shugaba Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekarar 2015.

Daya daga cikin dalilan da Trump ya bayar na daukar matakin shi ne cewar, yarjejeniyar bata shafi takaita shirin Iran na ci gaba da kera makamai masu linzami ba, sai kuma rage tasirinta a siyasar yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.