Isa ga babban shafi
Amurka

An damfari dattijai miliyan 2 a Amurka cikin shekara 1

Jami'an tsaron Amurka sun kame mutane 20 bisa zarginsu da hannu wajen damfarar dubban 'yan kasar.
Jami'an tsaron Amurka sun kame mutane 20 bisa zarginsu da hannu wajen damfarar dubban 'yan kasar. AFP Photo/Ali al-Saadi

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, ta gano cewa dattawa miliyan biyu aka zalunta a kasar, ta hanyar damfararsu dalar Amurka miliyan 750 a shekarar da ta gabata, ciki har da dabarun damfara ta wayoyin tarho na gaibu daga kasar India.

Talla

Jami’an tsaro dai na naci gaba da kokawa bisa karuwar matsalar ta damfarar masu yawan yawan shekaru, da suka ce babbar matsala ce a duniya, kasancewar ana samun haka a Birtaniya, Canada da Jamus.

Hanyoyin da bata gari kan bi wajen damfarar masu yawan shekarun sun hada da yi masu albishir da samun wani taimako, wanda aka samu rahoton aukuwar hakan a Amurka sau dubu 142 cikin shekarar data gabata.

A wani zubin bata garin kan bude shafi ne na musamman a yanar gizo, sai dai abinda mafi akasarin wadanda ake cuta basu sani ba, shi ne shafin na ‘yan damfara ne.

Wasu kuma kan rika buga waya ne kai tsaye ga mutun da yi masa albishir har da bashi lambar waya amma ta gaibu.

Zuwa yanzu dai jami'an tsaron Amurka sun kame mutane 20 bisa zarginsu da hannu wajen tafka wannan barna ciki harda wasu 'yan kasar India 2, amma babu karin bayani kan kasashen da sauran suka fito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.