Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta fara bincike kan bakar akwatin Ethiopian Airlines

Bakar akwatin jirgin Ethiopian Airlines kirar Boeing 737 MAX 8 da ya yi hadari tare da hallaka mutane 157
Bakar akwatin jirgin Ethiopian Airlines kirar Boeing 737 MAX 8 da ya yi hadari tare da hallaka mutane 157 REUTERS/Philippe Wojazer/File Photo

Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines ya ce ya mikawa Faransa bakar akwatin jirginsa kirar Boeing 737 MAX da ya yi hadari makon jiya tare da hallaka mutane 157, don ta gudanar da binciken da ya kamata, dai dai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da jingine amfani da nau’in jirgin samfurin Amurka.

Talla

A safiyar yau Juma’a ne tawagar jami’an kamfanin na Ethiopian Airlines suka isar da bakar akwatin jirgin ga hukumar kula da musabbabin faruwar hadurran jiragen sama ta Faransa BEA da ke birnin Paris don gudanar da binciken musabbabin hadarin na makon jiya.

Babban aikin hukumar ta BEA a yanzu shi ne tattara bayanan da ke cikin bakar akwatin jirgin kirar Boeing 373 MAX samfurin Amurka, wanda ta nan ne za ta tabbatar da hakikanin dalilan da suka haddasa masa hadari.

Kamfanin na Ethiopian Airlines ya ce ba ya da kwarewa tare da na’urorin gudanar da aikin binciken kan bakar akwatin jirgin da ya gano, matakin da ya ce hakan ya sanya shi mika aikin ga Faransa, wadda na cikin manyan kasashen duniya da suka dakatar da amfani da nau’in jirgin baya ga haramta masa keta sararin samaniyarsu.

A Larabar da ta gabata ne, Amurka ta ce ta gano kamanceceniya tsakanin dalilan da suka haddasa hadarin jirgin Lion Air na Indonesia wanda ya hallaka mutane 189 da kuma jirgin na Ethiopia da ya hallaka mutane 157, dukkaninsu kirar Boeing samfurin kasar ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.