Isa ga babban shafi
Amurka

Rabin Amurkawa ba sa goyon bayan tsige Donald Trump - Rahoto

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Yuri Gripas

Sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Amurka, ya nuna cewa rabin Amurkawa, basa goyon bayan tsige shugaban kasar Donald Trump, inda wasu ke cewa masu yi masa hassada ne kawai suka sanya shi a gaba.

Talla

Binciken ra’ayoyin jama’ar da Jaridar USA Today da kuma Jami’ar Suffolk suka gudanar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake kawo karshen binciken da kwamitin Robert Muller ke jagoranta game da rawar da kasar Rasha ta taka a zaben Amurka da ya gabata.

Kididdigar ta nuna cewa tun a watan 10 na shekarar da ta gabata aka samu koma baya game da neman ‘yan majalisar wakilan Amurka su tsige Shugaba Trump.

Duk da haka dai kididdigar ta nuna cewa kashi 52% na jama’a suna da shakku ko kuma ma babu, dangane da musanta zargin da shugaban keyi cewa Rasha ba ta da hannu a harkar zabensa.

Masu binciken sun ce shekara daya da ta gabata kashi 57% na jama’a ke da shakku game da karyata zagin da Trump yayi ta yi.

Tuni Robert Muller da ke wannan aiki na bincike ya ya dulmuya mutane 34 a zargin Rasha na da hannu wajen zaben Amurka, cikinsu kuma akwai jami’an leken asirin Rasha da wasu na hannun daman Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.