Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta sha alwashin hana hukuncin kisa kan wasu 'ya'yanta 3

Wasu dakarun sojin Iraqi, bayan kama wani da suke zargi da zama mayakin kungiyar IS.
Wasu dakarun sojin Iraqi, bayan kama wani da suke zargi da zama mayakin kungiyar IS. Reuters

Gwamnatin Faransa ta ce za ta dauki matakan hana Iraqi zartas da hukuncin kisa kan wasu Faransawa 3 da aka yankewa hukuncin rataya, bayanda aka kamasu a matsayin mayakan kungiyar IS.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce, za ta dauki matakan hana zartas da hukuncin ne, saboda adawar da take yi da aiwatar da hukuncin kisa a ko da yaushe da kuma ko ina.

A ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu wata kotun Iraqi ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan mayakan na IS 3 da aka kama su a Syria, wadanda suka kasance Faransawa.

Mutane ukun, na daga cikin Faransawa 13 da aka kama a Syria, daga bisani kuma aka mikasu ga gwamnatin Iraqi, bisa zarginsu zama mayakan kungiyar IS.

A halin yanzu, Faransawan da aka yankewa hukuncin kisan na da damar daukaka kara nan da wa’adin kwanaki 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.