Isa ga babban shafi
Poland

Tsananin zafi ya haddasa nutsewar mutane 150 cikin ruwa a Poland

Hukumomi a kasashen biyu sun ce galibi mutanen kan je wanka ne da nufin samun sauki daga tsananin zafin da nahiyar ke fuskanta
Hukumomi a kasashen biyu sun ce galibi mutanen kan je wanka ne da nufin samun sauki daga tsananin zafin da nahiyar ke fuskanta reuters

Akalla mutane 150 hukumomin kasar Poland da Lithuania suka tabbatar da nutsewarsu a ruwa a kokarinsu na samun sauki daga tsananin zafin da yankin Turai ke fuskanta dai dai lokacin da wani hasashe ke nuna za a iya ci gaba da fuskantar zabin na dan wani lokaci a nan gaba.

Talla

Ma’aikatar tsaro a kasar ta Poland ta bayyana cewa, babu wata rana da ta zo ta shude cikin watan Yuni ba tare da an samu wanda ya nutse a ruwa sanadiyyar tsananin zafin ba, inda ta ce galibin masu nutsewar maza ne.

Yayin zantawar mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron ta Poland, Bozena Mysocka da kamfanin dillancin labaran Faransa, ya bayyan acewa a jiya lahadi abin ya fi tsananta inda adadin mutane 10 suka nutse a ruwa.

A cewar Mysocka, kididdigarsu ta nuna cewa, adadin mutane 113 ne suka nutse a cikin ruwan tun bayan fara fuskantar tsananin zafin a Nahiyar Turai, wanda kuma ya ce shi ne mafi muni da kasar mai yawan jama’a miliyan 38 ta taba fuskanta a tarihi.

A bangare guda ita hukumar kashe gobara a Lithuania ta ce akwai adadin mutane 32 da suka nutse a ruwa sanadiyyar zafin wanda kuma ya faru ne saboda yadda su ke zuwa bakin ruwa wanka don samun sauki daga tsananin zafin.

Zafin da Poland ta fuskanta dai ya kai digiri 38 da digo 2 a ma’anin Salsiyas yayinda Lithuania ta fuskanci zafi mai karfin digiri 35 da digo 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.