Isa ga babban shafi
Turai-Asiya

Faransa ta mayarwa Pakistan kayayakin tarihi kusan 450

Kayan tarihi  da aka nuna a wani biki
Kayan tarihi da aka nuna a wani biki RFI/Isabelle Le Gonidec

Kasar Faransa ta mikawa Pakistan kayayakin tarihi kusan 450, wasun su da akayi su tun a karni na 4 da hukumomin kwastam suka kwace sama da shekaru 10.

Talla

Hukumar kwastan a tashar jiragen Charles de Gaulle dake birnin Paris ta kwace kayayakin a shekarar 2006 lokacin da ake kokarin safarar su.

Bayan binciken da hukumomi suka yi da kuma kai samame gidajen aje kayan tarihi a Paris, anyi nasarar kwace irin wadanan kayan tarihi 445 wanda aka mikawa jami’an diflomasiyar Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.