Isa ga babban shafi
Faransa-Saudiya

'Yar sarkin Makka ta gurfana a kotun Faransa kan dukan ma'aikacinta

Gimbiya Hassa bint Salman, 'yar uwa yarima mai jiran gado na Saudiya na Saudiya Muhammad bin Salman
Gimbiya Hassa bint Salman, 'yar uwa yarima mai jiran gado na Saudiya na Saudiya Muhammad bin Salman Arab.com

Hukumomin Kasar Faransa sun gurfanar da 'yar uwar Yarima Muhammad bin Salman a gaban kotu saboda tuhumar da ake mata na dukan wani ma’aikacin da ke mata gyara a gidan ta na alfarma da ke birnin Paris.

Talla

Ana tuhumar Gimbiya Hassa bin Salman wadda ‘ya ce ga Sarki Salman bin Abdulaziz da sanya mai tsaron lafiyar ta Rani Saidi da dukar Ashraf Eid lokacin da aka same shi ya na daukar hotan katafaren gidan a shekarar 2016.

Hassa dai ba ta gurfana a kotu ba yayin sauraren karar, amma lauyan ta ya ce taki amincewa da tuhumar da ake mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.