Isa ga babban shafi
Jamus

Merkel ta caccaki Trump kan nuna wariyar Jinsi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ®German Chancellor Angela Merkel speaks during Manfred Weber's,

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi tir da kalaman wariyar jinsi shugaba Donald Trump akan yan Majalisun kasar guda 4, inda ta ke cewa matakin ya sabawa abinda ya daga darajar Amurka.

Talla

Merkel ta nesanta kan ta daga kalaman shugaban inda ta bayyana goyan bayan ta ga Yan Majalisun.

Ita ma Firaministan Birtaniya Theresa May ta bayyana kalaman shugaba Trump a matsayin abinda ba za’a amince da shi ba, yayin da takwarar ta ta New Zealand Jacinda Arden tace ita ma bata goyan bayan kalaman.

A bangare daya kuma, 'yar Majalisa Ilham Omar ta samu gagarumar tarbo da ta koma mazabar ta, inda ta  ke cewa ba za ta sauya matsayi kan sukar manufofin shugaba Donald Trump ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.