Isa ga babban shafi

EU ta zabi Kristalina Georgieve don shugabantar IMF

'Yar takarar neman shugabancin asusun bada lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva
'Yar takarar neman shugabancin asusun bada lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva Yasuyoshi CHIBA / AFP

Ministocin kasashen kungiyar Tarayyar Turai, sun amince da Kristalina Georgieve babbar jami’a ta biyu a bankin duniya ‘yar kasar Bulgaria, a matsayin ‘yar takararsu daya tilo da ke neman mukamin shugabancin asusun bada lamuni na duniya IMF.

Talla

Bayan zaben da aka shafe tsawon dare ana gudanarwa, Kristalina da dara takwarorinta da yawan kuri’u baya ga zarra a cancanta, kuma matukar nadin na ta ya tabbata za ta zamo mace ta biyu da ta jagorancin asusun na IMF bayan Christine Lagarde wadda yanzu ta koma mukamin shugabar bankin Tarayyar Turai.

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ministan kudin Faransa, Bruno Le Maire ya ce ‘yar takararsu guda daya bayan zaben da ya gudana ita ce Kristalina kuma suna fata ta zamo magajiyar Lagarde.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.