Isa ga babban shafi

'Yan sanda sun kame mutum 600 cikin masu bore a Rasha

Arangamar masu zanga-zangar da jami'an tsaro a Rasha
Arangamar masu zanga-zangar da jami'an tsaro a Rasha REUTERS/Maxim Shemetov

Akalla mutane 600 jami’an ‘yan sandan Rasha su ka kame daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnati daga jiya Asabar zuwa yau Lahadi, boren da ke zuwa bayan da bangaren adawa ya sake kiran wani gangami don kalubalantar matakin gwamnati na hana su shiga zaben ‘yan majalisun kasar na watan Satumba.

Talla

Cikin sanarwar da bangaren adawar ya fitar ya bayyana cewa, kamen da jami'an tsaron kasar ke yi ba zai hana su fitowa don neman 'yancinsu ba.

Yayin zanga-zangar dai an samu arangama tsakanin jami'an tsaron da farar hula kwatankwacin wanda ya faru a makon jiya.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, bangaren adawar ya gaza samun izinin gudanar da zanga-zanga daga hukumomin kasar ne, matakin da ya tilasta masa kiran haramtacciyar zanga-zangar wadda ta kai ga kame mutum dubu 1 da dari 4 a makon jiya baya ga jikkata wasu da dama.

Cikin wadanda aka kama a cewar masu sanya idanu kan zanga-zangar a birnin Moscow har da ‘yan Jaridu 6 yayinda farar hula da dama suka samu munanan raunuka a kokarin jami’an tsaro na cafke su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.