Isa ga babban shafi

Watan Yulin 2019 shi ne mafi tsananin zafi a tarihin duniya- rahoto

Tsananin zafin na watan na Yuli ya dara duk wani zafi da duniya ta fuskanta a shekarun baya-bayan nan a cewar rahoton
Tsananin zafin na watan na Yuli ya dara duk wani zafi da duniya ta fuskanta a shekarun baya-bayan nan a cewar rahoton REUTERS/Pascal Rossignol

Wasu alkaluma da Cibiyar tauraron dan adam na Tarayyar Turai ta fitar a yau Litinin, sun bayyana watan Yuli a matsayin mafi tsananin zafi da duniya ta taba fuskanta a tarihi, sama da tsananin zafin shekarar 2016, wanda masana ke alakantawa da rashin daukar matakan magance matsalar sauyin yanayi.

Talla

Sanarwar da sashen kula da sauyin yanayi a Tarayyar Turai ya fitar a yau, ya ce duk da kasancewar bisa al’ada watan na Yuli na matsayin mafi zafi tsakan-kanin sauran watannin shekara amma a wannan karon zafin yafi tsananta fiye da kowanne lokaci.

Jean-Noel Thepaut shugaban sashen yanayi na Tarayyar Turai, ya ce yanayin kwayoyin zafin da suka sauka a sararin duniya ya dara wanda aka saba samu musamman a yankin Arctic da ke gabashin nahiyar Turai da aka fi fuskantar tsananin sanyi.

Alkaluman tauraron dan adama din na Nahiyar Turai, ya bayyana cewa ko da yankin Asiya da Afrika wadanda ke fuskantar zafi, zafin da suka samu a watan Yuli yayi tsananin da suka jima basu gani ba, tun bayan shekarun 1981 zuwa 2010.

Rabon da nahiyar Turai ta fuskanci tsananin zafi irin na watan Yulin a cewar alkaluman tun bayan tsananin zafin watan Yulin shekarar 2016 wanda bayanai ke cewa akwai tazarar digo 4 tsakanin zafin na shekarar 2016 da na 2019.

Tsananin zafin daim asana na ci gaba da alakanta shi da rashin daukar matakan magance matsalar dumamar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.