Isa ga babban shafi

An gano maganin cututtukan zuciya a birtaniya

Likita na duba mai cutar hawan jini
Likita na duba mai cutar hawan jini Medical Xpress

Wani binciken masana kiwon lafiya a birnin London na kasar Birtniya, ya gano wani sabon maganin hawan jinin da ke gaggautar saukar da jini baya ga magance matsalolin da suka shafi ciwon zuciya da akalla kashi 50 cikin dari.

Talla

Sabon maganin wanda aka sanyawa suna Polypill jaridar lafiya ta Lancet ta bayyana cewa tsawon shekaru 20 kenan da samar da shi sannan aka fara gwajinsa a tsakankanin shekarun 2011 zuwa 2013 kafin fara amfani da shi a bana.

Cikin tarin mutane masu fama da matsalolin da ke da alaka da ciwon zuciya ko hawan jini da suka yi amfani da maganin kamar yadda aka umarce su, bayanai sun nuna cewa sun samu raguwar hawan jini da akalla kashi 70 yayinda masu fama da bugun zuciya ya ragu da kashi 57.

A cewar Farfesa Kausik Ray na kwalejin Imperial da ke birnin London tsawon lokaci an dakatar da gwajin maganin kan mutane masu tarin yawa har zuwa lokacin da aka kammala gwaje-gwaje a bana.

Farfesa Ray ya bayyana cewa sabon maganin na saukar da hawa jinin nan take fiye da aikin da tsaffin magungunan na hawan jini da ciwon zuciyake yi a kwanaki 90.

Wasu rahotanni sun nuna cewa farkon gwajin maganin na Polypill ya gudana ne kan wasu mutane dubu 7 masu shekaru tsakanin 50 zuwa 75 can a yankin Golestan na kasar Iran karkashin jagorancin Dr Reza Malekzadeh na jami’ar kimiyya da ke birnin Tehran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.