Isa ga babban shafi

'Yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da taron G7 a Faransa

Masu zanga zangar adawa da taron G7 wanda ke gudana a birnin Biarritz na kudancin Faransa.
Masu zanga zangar adawa da taron G7 wanda ke gudana a birnin Biarritz na kudancin Faransa. REUTERS/Stephane Mahe

Jami’an ‘yan sandan Faransa sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye kan dandazon masu zanga-zangar adawa da taron G7 wanda kasar ke karbar bakonci a Biarritz, gari mafi yawan masana’antu da ke kudancin kasar.

Talla

Sama da mutane dubu 9 ne dai ciki har da masu rajin kare muhalli, da kuma masu adawa da tsarin mulkin jari hujja suka tsunduma zanga-zangar a yammacin jiya Asabar don nuna adawa da taron kasashen na G7.

Cikin muhimman bukatun masu zanga-zangar kuma akwai daukar matakan gaggawa wajen kawo karshen gobarar dake barazanar nakasa dajin Amazon, sai kuma cika alkawuran manyan kasashen na yakar matsalar sauyin yanayi ko dumamarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an 'yansandan sun rika harba hayaki mai sanya hawayen kan dandazon masu zanga-zangar da suke rufe manyan tituna don nuna adawa da taron, wanda suka bukaci lallai ya samar da mafita game da gobarar dajin Amzon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.