Isa ga babban shafi

Boris Johnson ya sha alwashin kulla yarjejeniya kafin ficewar Birtaniya

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson Danny Lawson/PA Wire/Pool via REUTERS

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sha alwashin ganin ya kulla sabuwar yarjejeniya da EU gabanin wa’adin ficewar kasar daga Tarayyar Turai, matakin da ya ke zuwa bayan kayen da ya sha yayin kuri’ar da aka kada kan batun yayin zaman majalisar kasar a yau Laraba.

Talla

Firaminista Boris Johnson wanda ya sha kaye bayan fuskantar kakkausar suka kan kudirinsa na kiran zabe gabanin ficewar, ya ce zai yi kokarin kulla sabuwar yarjejeniyar da za ta samu karbuwa a Birtaniyar.

A cewar Johnson wanda matakinsa na kulle majalisar kasar ke ci gaba da tayar da hazo musamman daga bangaren jam’iyyar adawa, ya ce yayin taron EU da zai gudana a Brussels cikin wata mai zuwa zai yi kokarin kulle yarjejeniya da wakilcin kungiyar gabanin ficewar ko da dai ya ce har yanzu yana kan bakansa na ficewar ko da ba tare da yarjejeniya ba.

Firaministan na Birtaniya, ya zargi bangaren jam’iyyar Labour da kitsa manakisar da ta kai ga kin amincewar majalisar da kudirinsa na gudanar da zabe.

Gabanin zaman Majalisar na yau Laraba dai, Johnson sai da ya yi wani zama na musamman da ministocinsa don ganin ya samu goyon baya kan kudirin na sa na kiran sabon zabe, haka zalika ya yi makamanciyar ganawar da shugabar yankin na Arewacin Ireland.

Tuni dai masana tattalin arziki ke ci gaba da gargadin kasar kan illar da ficewar za ta haifarwa kasar ta fuskar tattalin arziki dai dai lokacin da matsalar adadin marasa aikin yi ke ci gaba da karuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.