Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sallami mashawarcinsa kan tsaro

John Bolton,mai baiwa shugaban Amurka shawara kan tsaro
John Bolton,mai baiwa shugaban Amurka shawara kan tsaro REUTERS/Peter Nicholls/File Photo

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sallamar mai ba shi shawara kan tsaro mai tsatsauran ra’ayin nan, John Bolton, yana mai cewa tasu bata zo daya ba game da rikicin da ake samu kan manufofin hulda da kasashen wajen Amurka.

Talla

Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya bukaci takarda ajiye aiki daga gun Bolton kuma ya mika mai, yana mai cewa a mako mai zuwa zai bayyana wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai Trump wanda dama an shirya zai yi taron manema labarai a fadar White House kasa sa’o’i biyu bayan labarin sallamar sa ya musanta batun cewa tsige shi aka yi, inda ya nace cewa shi ya yi murabus don kashin -kansa

Labarin sallamar wanna kusa na gwamnatin Amurka na zuwa ne kwanaki bayan Trump ya tayar da kura ta wajen bayyana cewa ya soke duk wata tattaunawar sirri da suke da Kungiyar Taliban na Afghanistan, lamarin da ya ba da mamaki a Amurka.

Bolton dai tsohon soja ne mai wuyan sha’ani, wanda ake danganta shi da mamayar Iran da Amurka ta yi da ma wasu tsauraran matakai da kasar ta dauka a harkokinta da kasashen waje.

Ana mishi ganin daya daga cikin wadanda suka zafafa lamari har Amurka ta ke daukan tsauraran matakai kan Iran da Venezuela da sauran wuraraen da ake rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.