Isa ga babban shafi
Faransa

Wasu Faransawa na fuskantar tuhuma kan wulakanta hoton Macron

Shugaba Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel Macron . Yoan Valat/Pool via REUTERS

A Faransa, an soma zaman shara’ar wasu mutane da ake tuhuma da laifin cire hotunan Shugaban kasar Emmanuel Macron, a wani shirin su na nuna gazawar Shugaban dangane da yaki da dumamar yanayi.

Talla

Mutanen wadanda suka kunshi masu rajin kare muhalli da wani mai daukar bidiyo ana tuhumarsu ne da laifin cire hotunan Shugaba Emmanuel Macron a wasu da’irorin babban birnin kasar, a wani shirinsu na nuna gazawar Shugaban wajen magance matsalar dummamar yanayi.

Mutanen su 8 wadanda shekarunsu ya fara daga 23 zuwa 36, yanzu haka su na tsare hannun mahukunta bayan da aka samu tabbacin su ke da hannu wajen tsige hotunan shugaban a ranar 21 da 28 ga watan Fabrairun da ya gabata bayan da suka kutsa kai cikin da’irorin karamar hukuma ta biyar, da ta uku da kuma ta hudu suka ciccire hotunan shugaba Macron.

Rahotanni sun bayyana cewa yayinda su ke aikin ciccire hotunan shugaban mutanen sun rika daukar bidiyon abin da su ke aikatawa inda suka yada shi a wani shafi mai zaman kansa.

Karkashin dokar Faransa dai dole ne mutanen su fuskanci hukuncin hukuma.

Tuni dai shirin cire hotunan Shugaba Macron ya samu karbuwa a wasu yankuna na Faransar ciki har da birnin Paris.

A wani lisafin da wata kungiya mai zaman kanta da ke nisanta kan ta daga tashin hankali Mouvement Action Non Violente Cop 21 ta tattara akalla hotunan shugaban kasar da aka bale 128.

Baya ga haka kungiyar ta bayyana cewa wasu magoya bayan ta 57 na fuskantar tuhuma daga kotu, biyo bayan samun su da laifin cire hotunan Shugaban kasar, wanda a hukumance za su iya fuskantar dauri na shekaru 5 tare da biyan tarar Yuro dubu 75.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.