Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ba za ta tattauna da Amurka ba

Shugaban Iran,Hassan Rouhani
Shugaban Iran,Hassan Rouhani AP

Iran ta ce ba ta da wani shirin tattaunawa da Amurka yayin taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, kalaman da ke matsayin martani ga Amurka da ta bayyana cewa akwai yiwuwar tattaunawa tsakanin Donald Trump da Hassan Rouhani, dai dai lokacin da kassahen biyu ke sake fuskantar rikici game da harin Houthi kan cibiyoyin man Saudiya.

Talla

Matakin kawar da tattaunawar na Iran na zuwa ne a dai dai lokacin da kassahen Turai ke fatan ganin an samu saukin rikicin da ke tsakanin kasashen biyu tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar Nukiliyarta, Yayin da a bangare guda sabon rikici game da hari kan matatun man Saudiya ya barke tsakanin bangarorin biyu, ko da yake duk da haka Amurkan ta ce tana duba yiwuwar ganawar.

Kafin yanzu dai Amurka ta ce za ta dauki tsauraran matakai kan Iran wadda ta zarga da kitsa harin kan Saudiya, sai dai a Litinin din nan shugaba Donald Trump ya ce baya tunanin daukar matakin Soji kan Iran game da harin.

A cewar Donald Trump akwai nauye-nauye da rikice-rikice masu tarin yawa akan Amurkan, inda cikin sakonsa na Twitter Trump ya ke cewa yanzu ya na jiran matakin da Saudiya za ta dauka da kuma wanda ta ke zargi da kaddamar da harin, bayan da Iran ta musanta hannu a hari kan cibiyoyin man na Saudiya da aka zarge ta.

Tuni dai kasashen Rasha da China da kuma Tarayyar Turai suka bukaci kai zuciya nesa tsakanin kasashen na Saudiya Iran da kuma Amurka, dai dai lokacin da farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya bayan da Saudiyar ta dakatar da kashi 50 cikin 100 na man da ta ke fitarwa bayan farmakar cibiyoyin man na ta mafi girma a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.