Isa ga babban shafi
Faransa

Iyalan mayakan jihadi sun kai ministan harkokin wajen Faransa kotu

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic MARIN / AFP

Mata da ‘yayan Faransawa da dama mayakan jihadi da ke Syria sun shigar da karar ministan harkokin wajen Faransa, Jean – Yves Le Drian sakamakon hana su shigowa kasar.

Talla

Ana zargin ministan harkokin wajen Faransan ne da kasa samar da taimako ga mutanen da ke cikin hadari a sansanonin da ke karkashin kulawar dakarun Kurdawa a arewa – maso – gabashin Syria a karar da aka shigar a watan Yuli da Satumba.

An shigar da wannan kara ne gaban babban kotu ta musamman da ke sauraron korafe – korafe kan ministoci da suka yi murabus da ma wadanda ke kan aiki.

Wannan ne kalubalen shari’a na baya – bayan nan da Faransa ke fuskanta dangane da adawar da ta dade tana yi da batun barin ya’ya da matan wadanda ake zargin mayakan jihadi ne a Iraqi ko Syria su koma gida.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin Faransan , wacce ta ce tana la’akari ne da bukatun da aka shigar gabanta daya bayan daya, ko kuma bisa mahimmancinsu, yara 17 ne kawai ta maido gida tun a watan Maris, wadanda akasarinsu marayu ne.

Masu lura da al’amuran da ka je ya dawo, sun ce wannan manufa ta gwamnatin Faransa ta jefa wadannan mutane da ba su aikata ba – daidai ba cikin matsananncin damuwa da tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.