Isa ga babban shafi
Faransa

Mummunar gobara ta tashi a masana'antar sarrafa sinadarai

Wani sashi na masana'antar sarrafa sinadaran Faransa dake birnin Rouen, bayan tashin gobara. 26 ga Satumba, 2019.
Wani sashi na masana'antar sarrafa sinadaran Faransa dake birnin Rouen, bayan tashin gobara. 26 ga Satumba, 2019. Blas Garcia Photography via REUTERS / MANILA BULLETIN

Wata mummunar gobara ta barke da safiyar yau Alhamis a wata masana’antar sarrafa sinadarai dake birnin Rouen a arewacin kasar Faransa.

Talla

Babu Karin bayani kan adadin wadanda gobarar ta rutsa da su ko kuma barnar da ta tafka.

Sai dai akwai fargabar cewa, gobarar ka iya haddasa gurbacewar ruwa kogin Seine dake kusa da masana’antar.

Jami’an kwanakwana kimanin 130 suka dukufa wajen kokarin kashe gobarar, yayinda jami’an tsaro suka yiwa masana’antar kawanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.