Isa ga babban shafi
Turai-Birtaniya

Birtaniya za ta sake mikawa EU bukatar kulla sabuwar yarjejeniya

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson Parliament TV via REUTERS

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya ce yana gaf da mika tayin kulla sabuwar yarjejeniyar rabuwa da kungiyar kasashen Turai EU, duk da gargadin wasu kasashen Turan a baya bayan nan, kan cewa abu ne mawuyaci a cinma wata matsaya.

Talla

Wannan alwashi na Firaminista Boris Johnson ya zo ne yayinda ya rage kasa da kwanaki 30, wa’adin kammala ficewar Birtaniya daga cikin EU ya cika a ranar 31 ga watan Oktoban da muka shiga.

Sai dai a nasu bangaren shugabannin kungiyar kasashen Turan sun ce babu wasu alamu ko kuma kwarin gwiwar cewa Birtaniyar za ta gabatar da tayin yarjejeniyar rabuwarsu sama da wadda ke kasa, da suka cimma da tsohuwar Fira Minista Theresa May.

A baya bayan nan ne dai, Boris Johnson ya sha kaye a kotu, bayan da ta soke umarnin da ya bayar na dakatar aikin majalisar Birtaniya, har sai ya rage makwanni biyu wa’adin ficewar su daga Turai ya cika, abinda wasu ke kallo da kokarin tabbatar da aniyarsa ta jagorantar rabuwa da EU ba tare da Yarjejeniya ba, abin da masana tattalin arziki suka yi gargadin ba zai yiwa kasar kyau ba.

A yau Talata kamfanin kera motoci na Nissan ya ce ficewar Birtaniya daga EU babu yarjejeniya tilasta masa janye ayyukan kera sabbin nau’ikan motocinsa, abinda zai haddasa hasarar dubban guraben ayyukan yi ga ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.