Isa ga babban shafi
Faransa

Mutumin da ya daba wa 'yan sanda wuka a Faransa mai tsatsauran ra'ayin addini ne

Shelkwatar 'yan sandan Faransa a tsakiyar birnin Paris
Shelkwatar 'yan sandan Faransa a tsakiyar birnin Paris BERTRAND GUAY / AFP

Wani mai gabatar da kara kan a bin da ya shafi ayyukan ta’addanci a Faransa ya ce mutumin nan da ya farmaki abopkan aikinsa da wuka a shelkwatar ‘yan sanda har ya yi sanadin mutuwar mutum 4 a cikinsu yana riko ne da akida irinta masu ‘tsatsauran ra’ayin addinin Islama’.

Talla

Dan shekara 45 din wanda kwararre ne a sha’anin komfuta yana dasawa da ‘yan Salfiya, wadanda ake wa kallon masu tsatsauran ra’ayi daga cikin ‘yan Sunni, kuma ya sha kare ta’asa da ake aikatawa da sunan addinin Musulunci.

Jami’en ‘yan sanda 4 ne ciki har da mace guda suka mutu a harin na ranar Alhamisa shelkwatar ‘yan sanda kusa da majami’ar Notre Dame a tsakiyar birnin Paris.

‘Yan sanda sun harbe maharin, mai suna Mickael Harpon har lahira.

Wanna lamari dai ya razana illahjirin rundunar ‘yan sandan Faransa wanda tun dafarko suke korafi kan rashin ba su kwarin gwiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.