Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai ci gaba da aiwatar da dokokin fansho

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Charles Platiau

Shugaban  Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin cigaba da aiwatar da sauye sauyen sabon kudin fansho duk da adawar da kungiyoyin kwadao a kasar keyi.

Talla

Ganin yadda kungiyoyin kwadago daban daban ke gudanar da yajin aiki domin nuna rashin amincewar su da shirin sauya dokar fanshon da gwamnatin kasar ke yi, shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewar babu abinda zai hana shi cimma kudirin sa na yi wa dokar gyara.

Yayin hira da gidan rediyon RTL, Macron yace ko da shirin na sa zai rage masa farin jini a hannun Faransawa, zai cigaba da jajircewa har sai ya ga nasarar sa.

Manyan kungiyoyin kwadago sun kira gagarumar zanga - zanga ranar 5 ga watan Disamba mai zuwa domin sake nuna adawar su da shirin, matakin da ake ganin zai durkusar da harkokin sufuri da kuma harkokin yau da kullum.

Shirin shugaban zai hade harkokin fanshon kungiyoyin ma’aikata 42 da ke kasar da kuma sanya lokacin ritaya daga aiki zuwa shekaru 64 domin samun cikakken fansho da kuma 62 ga masu samun takaitaccen fansho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.