Isa ga babban shafi
Amurka

Kallo ya koma kan Dattijai dangane kudurin tsige Trump - Pelosi

Nancy Pelosi, shugabar majalisar wakilan kasar Amurka.
Nancy Pelosi, shugabar majalisar wakilan kasar Amurka. REUTERS/Jonathan Ernst

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta ta bayyana larabar nan a matsayin ranar da za su kada kuri’a kan bukatar tura kudurorin tsige shugaban kasar Donald Trump zuwa majalisar Dattijai.

Talla

Wannan matakin dai shi ne na karshe da zai tilastawa shugaba Trump gurfana gaban ‘yan majalisar dattijai, domin fuskantar tuhume-tuhumen da ake masa na gayyatar Ukraine ta yi katsalandan a zabukan Amurka, da kuma amfani da karfin ikonsata hanyar da bata dace ba.

Yayin karin bayani a Shafinta na Twitter, Pelosi ta ce a halin yanzu kallo ya koma kan ‘yan majalisar dattijai don ganin yadda za su zabi bangaren kundin tsarin mulkin kasa, ko kuma rufa-rufa da aikata ba dai dai ba.

Wannan mataki da aka shiga, ya sanya Donald Trump zama shugaban Amurka na 3 a tarihi da zai gurfana gaban ‘yan majalisun kasar, bisa tuhumarsa da aikata laifukan da za su kai ga tsige shi daga karagar mulki.

Sai dai wasu magoya bayan shugaban harma da shi kansa, na ganin zai yi wahala kudurin tsige shin ya samu shiga a zauren majalisar dattijan, la’akari da cewar ‘yan jam’iyyarsa ta Republican ke da rinjaye da adadin 53, yayinda Democrats ke da 47, wanda kuma ana bukatar rinjayen kashi 2 bisa 3 ne kafin samun nasarar tsige shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.