Isa ga babban shafi
Amurka-Afghanistan

Amurka ta yi luguden bama-bamai sau dubu 7 a Afghanistan bara- rahoto

Wani yanki da Sojin Amurka suka farmaka a Afghanistan.
Wani yanki da Sojin Amurka suka farmaka a Afghanistan. REUTERS/Stringer

Wani rahoto ya bayyana cewa, Amurka ta yi luguden bama-bamai har sau dubu 7 da 423 a Afghanistan a bara kadai, alkaluman da aka bayyana a matsayin mafi muni cikin akalla shekaru 10 da Amurkan ke kaddamar da hare-harenta a kasar.

Talla

Rahoton wanda rundunar sojin saman Amurka ta fitar ya bayyana cewa, an samu karuwar luguden bama-baman ne bayan Washington ta kara kaimi wajen kaddamar da hare-hare a daidai lokacin da take kan tattaunawar janye dakarunta da mayakan Taliban.

Rundunar sojin saman ta wallafa wannan rahoton ne a shafin Intenet, inda bayanai ke nuna cewa, sabbin alkaluman bama-baman sun zarce wanda aka gani a shekarar 2009 a zamanin mulkin tsohon shugaban Amurka Barack Obama, lokacin da aka kaddamar da makamancin farmakin har sau dubu 4 da 147.

Tun bayan zaben Donald Trump a matsayin shugaban Amurka a shekarar 2016, kasar ta zafafa hare-haren bama-bamai a Afghanistan.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun sha bayyana damuwarsu kan yadda hare-haren na Amurka ke ci gaba da kassara da dama daga cikin fararen hula a kasar.

A farkon watanni shida na shekarar bara, dakarun da ke samun goyon bayan gwamnati tare da hadin guiwar sojojin Amurka, sun kashe fararen hula 717 a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.