Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai

Dubban 'yan Birtaniya da suka taru da safiyar Asabar don yib bankwana da Tarayyar Turai a birnin Landan.
Dubban 'yan Birtaniya da suka taru da safiyar Asabar don yib bankwana da Tarayyar Turai a birnin Landan. DANIEL LEAL-OLIVAS / AFP

Bayan shafe tsawon shekaru ana takaddama da gutsiri – tsoma, a Jumma’ar nan Birtaniya ta kawo karshen kasancewarta da kungiyar Tarayyar Turai da ta shafe shekaru kusan 50 tana cikinta, da zummar nema wa kanta makomar da masu lura da al’amura suka ce tana cike da rashin tabbas.

Talla

An gudanar da bukukuwa a wasu sassar kasar, bayan da kasar ta kasance ta farko da ta bar wannan kungiya da aka kafa don samar da hadin kai tsakanin kasashen Turan, bayan da suka sha radadin yakin Duniya na biyu.

Dubban mutane ne suka taru a dandalin majalisar dokokin na Birtaniya da misalin karfe 11 agogon GMT, don murnar yin hannun riga da Turai.

A Asabar dinnan, Birtaniyar ta fara tattaki zuwa makoma mai cike da rashin tabbas ba tare da Tarayyar Turai ba, sa’o’i bayan rabuwa mai dimbim tarihi da ya gamu da mabambamtan ra’ayoyi daga al’ummar kasar.

Kusan babu wani abin da zai sauya biyo bayan wannan hannu riga da Birtaniya ta yi da Tarayyar Turai, saboda janyewar gaba daya za ta dauki tsawon watanni 11 kamar yadda yake a kunshin yarjejeniyar.

Hakan na nufin ‘yan Bitrniya na iya aiki tare da gudanar da kasuwancinsu a kasashen da ke cikin Tarayyar Turai har zuwa ranar 31 ga watan Disamba na wannan shekarar, sai dai Birtaniya ba za ta samu wakilici a kungiyar ba daga yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.