Isa ga babban shafi

An bude masallacin farko a Slovenia bayan shekaru 50

Hoton Masallacin Christchurch
Hoton Masallacin Christchurch Reuters/路透社

Bayan kwashe shekaru 50 ana fuskantar matsaloli, an bude Masallachi na farko a babban birnin Slovenia, wato Ljubijana, wanda aka shirya gina shi shekaru 50 da suka gabata amma rashin kudi da kuma adawa suka haifar da tsaiko.

Talla

Cikin masu adawa da ginin harda wadanda basa goyan bayan taimakon gwamnatin Qatar wajen bada kudade da kuma wadanda suka jefa kana alade a cikin Masallachin da kuma zuba jinin sa domin hana ginin.

Shugaban al’ummar Musulmin kasar Mufti Nedzad Grabus ya bayyana Masallachin a matsayin wani gagarumin cigaba.

Slovenia ce kasa ta karshe daga cikin kasashen da suka fito daga tsohuwar Yugislavia da ta samu Masallachi a babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.