Isa ga babban shafi
Turai

Jam'iyyun siyasa na tattaunawa don kafa Gwamnati bayan zabe

Yar takara a jam'iyyar Sinn Fein Mary Lou McDonald a birnin  Dublin
Yar takara a jam'iyyar Sinn Fein Mary Lou McDonald a birnin Dublin RFI/Jan van der Made

Jam’iyyar Sinn Fein a kasar Ireland ta zama jam’iyya ta biyu mafi girma a Majalisar dokokin kasar, abinda zai bata damar shiga sabuwar gwamnati a dama da ita.Bayan kamala kidaya kuri’u jiya talata, Sinn Fein ta samu kujeru 37 daga cikin 160 dake Majalisar wakilai, a zaben da mutane sama da kasha 62 suka kada kuri’a.

Talla

Jam’iyyar Fianna Fail ke kan gaba da kujeru 38, yayin da Jam’iyyar Firaminista Leo Varadkar ta Fine Gael ke da kujeru 35 a Majalisar.

Tuni aka fara tattaunawa domin kafa sabuwar gwamnati.

Zaben ya kasance zakaran gwajin dafi ga Firaministan kasar tun bayan ficewar Birtaniya daga cikin gungun kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.