Isa ga babban shafi
Saudiya-Wasanni

Hukumar wasannin Saudiya ta kaddamar da gasar kwallon kafar mata

Wasu mata a Saudiya yayin shirin shiga kallon kwallon kafa a filin wasa na Sarki Abdullah dake birnin Jiddah.
Wasu mata a Saudiya yayin shirin shiga kallon kwallon kafa a filin wasa na Sarki Abdullah dake birnin Jiddah. AFP

Hukumar wasannin Saudiya ta kaddamar da gasar kwallon kafar mata a kasar da za ta kunshi ‘yan sama da shekaru 17.

Talla

Hukumar wasannin Saudiyan tace wasannin gasar kwallon kafar matan za su rika gudana ne a biranen Jiddah, Riyadh da kuma Dammam.

Wannan matakin dai shi ne na baya bayan nan da ake gani a kasar ta Saudiya dangane da sauye-sauyen sassauci kan lamurran da suka shafi mata, a karkashin jagorancin Yarima mai jiran gado Muhd bin Salman.

Kafin kaddamar da gasar kwallon kafar matan a Saudiya, sai da aka soma basu damar shiga filayen wasanni don kallon kafar kai tsaye a cikin watan Janairun shekarar 2018.

Wasu daga cikin sauye-sauyen da suka sahfi mata da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ya jagoranci samarwa a Saudiya, sun hada da basu damar yin tuki, da kuma yin tafiye-tafiye ba tare da muharrami ba.

A shekarun baya shugabannin Saudiya sun sha fuskantar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam dangane da tsarin dokokin da suka shafi lamurran mata, sai dai ga dukkanin alamu, a yanzu hukumomin na Saudiya na son yin amfani da fannin wasanni don sauya irin kallon da kungiyoyin na kare hakkin dan adam ke musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.