Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirsu ta kashe Faransawa kusan 900 a kwana guda

Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa
Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa JEAN-CHRISTOPHE VERHAEGEN / AFP

Faransa ta sanar da mutuwar karin mutane 833 a rana guda kadai, bayan kamuwa da cutar coronavirus, adadi mafi muni da kasar ta gani tun bayan barkewar wannan annoba a kasar.

Talla

Adadin ya kunshi mutanen da suka mutu a asibitoci da kuma gidajen kula da tsofaffi.

Ministan Lafiyar Faransa, Olivier Veran ya shaida wa manema labarai cewa, wannan sabon adadi na mamata, na nuni da cewa, har yanzu ba a shawo kan wannan annoba ba.

A jumulce dai, mutane dubu 8 da 911 ne coronavirus ta kashe a Faransa, yayin da kasar ta shiga mako na uku na aiwatar da dokar takaita zirga-zirgar jama'a da zummar dakile yaduwar annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.