Isa ga babban shafi
Wasanni

An dakatar da Morocco karbar bakuncin gasar cin Kofin Afrika

RFI Hausa

Hukumar kwallon Kafa ta Nahiyar Afruka ta dakatar da kasar Morocco kan batun karbar bakuncin gasar cin Kofin Nahiyar Afruka na 2015 da a baya aka shata cewar kasar ta Morocco ce za ta karbi bakuncin gasar

Talla

Yanzu dai Hukumar kwallon Kafar ta Afruka, ta tabbatar da cewar dai Morocco ba za ta dauki bakuncin gasar ba, saboda yadda ita kanta Morocco ke fargaba akan matsala Cutar Ebola da aka bayyana bulluwarta a wasu sassan kasar.

Hukumar CAF dai bata bayyana sabon bagiren da za’a gudanar da gasar ba, amma ana hasashen kasashe biyu wato Najeriya ko Afruka ta kudu, su kasance kasashen da mai yuwa a dora masu wannan alhakin.

Amma bayan da aka dage ita wannan gasar zuwa 2016, kasar Masar wadda aka yi bayyanawa a matsayin wadda ga alama na cikin na gaba gaba ga karbar bakuncin gasar ta ce ita kam ba za ta iya ba saboda matsalar tattalin arziki da Siyasa.

Suma dai kasashen Ghana da Afruka ta kudu, sun fidda kansu daga layin masu son daukar bakuncin gasar, a yayin da a Najeriya zaben shugabancin kasar da za’a gudanar zai zo ne akalla Mako daya bayan gasar, kuma ba’a san yadda zata kaya ba a sakamakon zaben lura da yadda al’ummar kasar ke dari-dari.

Akwai kasashe kamar Gabon da Equatorial Guinea, amma dukkaninsu filayen wasanni bibbiyu ne kadai suke da su.

Ita kuma Angola bata da isassun kudin da za ta shiryawa gasar, a yayin da Tunisia ke fama da tashin hankalin siyasa, amma Algeria ta ce za ta iya daukar bakuncin gasar a 2017.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.