Isa ga babban shafi
Senegal

Kotun Kolin Senegal ta tabbatar da hukunci da aka yanke wa Karim Wade

Karim Wade ya rike mukamai a zamanin mulkin Mahaifinsa
Karim Wade ya rike mukamai a zamanin mulkin Mahaifinsa AFP PHOTO / GEORGES GOBET

Kotun Kolin Senegal ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari, da aka yanke wa Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, kan laifin sama da fadi da kudaden jama’a.

Talla

Wannan dai babban koma-baya ne ga Karim wanda ke son a dama da shi ga harakokin siyasar kasar Senegal.

Kotun kolin ta yi watsi da karar da Karin Wade ya yi, inda ya nemi a sauya hukuncin na daurin shekaru 6, da tarar kudi har yuro miliyan 210, kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 230.

Cikin watan Maris aka yanke wa Karim Wade hukuncin, bayan da kotu ta same shi da tara dukiyar mai yawan gaske ta haramtacciyar hanya, a lokacin da ya ke rike da mukamin minista, lokacin mulkin mahaifinsa Abdulaye Wade.

Kotun ta kuma bada umarnin karbe kadarorin dan tsohon shugaban, da ya rike ma’aikatu daban daban a lokacin mulkin mahaifinsa.

Hukuncin ya haifar da rarrabuwar kanun ‘yan kasar, inda masu adawa da hukuncin na kotu suka yi ta zanga zanga a birnin Dakar.

Da yawa daga cikin ‘yan Senegal na nuna kyama ga Karim, Saboda dadewar da ya yi a Turai, inda kuma suka nuna mishi hakan karara ciki shekarar 2009 lokacin da ya yi takarar Magajin gari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.