Isa ga babban shafi
FIFA

Odegbami na Najeriya ya shiga takarar FIFA

Tsohon kaftin din Najeriya Segun Odegbami ya bayyana kudirinsa na shiga takarar neman kujerar shugabancin hukumar FIFA
Tsohon kaftin din Najeriya Segun Odegbami ya bayyana kudirinsa na shiga takarar neman kujerar shugabancin hukumar FIFA dailypost.ng

Tsohon kaftin din Najeriya Segun Odegbami ya bayyana kudirinsa na shiga takarar neman kujerar shugabancin hukumar FIFA da ke kula da sha’anin kwallon kafa a duniya.

Talla

Tsohon dan wasan na Najeriya wanda ya taba lashe kofin Afrika a 1980 ya bayyana kudirin shiga tsakarar ne a jiya Talata domin maye gurbin Sepp Blatter wanda zai yi murabus a watan Fabrairu.

Adegbami ya ce FIFA na bukatar wanda zai sauya hukumar musamman halin da ta ke ciki a yanzu.

Adegbami yanzu ya shiga sahun manyan jiga-jigan kwallo da ke neman kujerar shugabancin FIFA da suka hada da Michel Platini da attajirin Korea ta kudu Chung Mong-Joon.

Kuma yanzu ya mika kudirinsa ga hukumar kwallon Najeriya NFF domin samun goyon baya.

A ranar 26 ga watan Fabrairu ne za a gudanar da zaben a badi a birnin Zurich

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.