Isa ga babban shafi
Tennis

Djokovic ya lashe Australian Open

Dan kasar Serbia Djokovic
Dan kasar Serbia Djokovic REUTERS

Novak Djokovic na Serbia ya lashe kofin Australian Open bayan ya doke Andy Murray na Birtaniya a wasan karshe da suka fafata a jiya Lahadi.

Talla

Wannan ne karo na shida da Djokovic ke lashe kofin gasar, inda yanzu ya yi kafada da Roy Emerson na Australia wanda ya lashe kofunan gasar tsakanin 1961 zuwa 1967, nasarar da ba a sake samu ba a tsawon shekaru 49.

Yanzu kofuna 11 na Grand Slam Djokovic ya tara, sai dai yana bayan Roger Federer wanda ya lashe manyan kofunan Tennis 17.

Bangaren Mata

‘Yar kasar Jamus Angelique Kerber ce ta lashe kofin gasar Australian Open bayan ta doke jarumar Tennis ta duniya Serena Williams a karawar karshe da suka yi a ranar Assabar.

Wannan ne karon farko da Kerber ta lashe kofin gasar kuma wannan ne karo na farko da wata ‘Yar wasa daga Jamus ta lashe kofin Australian Open.

Sau shida Serena Williams na lashe kofin gasar Australian Open.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.