Isa ga babban shafi
Tennis

Kamfanoni sun nisanta kansu da Sharapova

Maria Sharapova ta Rasha
Maria Sharapova ta Rasha REUTERS/Gonzalo Fuentes/Files

Kamfanonin da ke hulda da Maria Sharapova ta Rasha sun fara nisanta kansu da ‘Yar wasan ta Tennis bayan ta fasa kwai akan tana shan kwayu masu sa kuzari.

Talla

Sharapova ta ce ta dade tana shan kwayar maganin Meldonium daya daga cikin kwayun da hukumar yaki da shan kwayu ta haramta a bana.

Amma ta yi nadama na rashin daina shan kwayar da Hukumar WADA ta saka cikin jerin kwayu masu sa kuzari a watan Janairu.

Kamfanoni irinsu Nike da Porsche sun katse hulda da Sharapova a yanzu.

Sharapova dai ta lashe kofin Gram slams guda biyar tare da lashe kofunan gasannin Tennis na WTA 35.

Sharapova dai na cikin jerin sahun attajiran ‘yan wasa a duniya.

Manyan ‘Yan wasa irinsu Serena Williams sun yaba da yadda Sharapova ta fito ta amsa cewa ta sha kwaya.

Shan abubuwa masu sa kuzari dai babbar matsala ce da ta shafi sha'anin wasanni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.