Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Serena ta fitar da Johanna Konta daga Australia Open

Serena Williams ta kai wasan dab dana karshe a Australia Open
Serena Williams ta kai wasan dab dana karshe a Australia Open REUTERS/Kevin Lamarque

Zakaran Tennis ta duniya Serena Williams ta fitar da Johanna Konta ta Britaniya a gasar Australia open bayan doke ta a wasan dab dana karshe da ci 6-2, 6-3.

Talla

Wannan ne haduwan Farko da Serena ke yi da Johanna, wacce ta yi fatan samun nasara kan Williams, amma hakan bai samu ba.

Da wannan nasara yanzu Serena mai shekaru 35 ‘yar Amurka da sau 6 tana daga Australia Open, za ta fuskanci Mirjana ta Croatia da ta doke Karolina ta Jamhuriyar Czaech.

Idan Serena ta lashe wannan kofi za ta kafa sabon tarihi lashe manyan kambuna 23 a duniyar Tennis.

A Fanin Maza

Roger Federer ya tsallake zuwa wasan dab dana karshe, wanda yazo wa dan wasan da mamaki, bayan shafe watanni 6 baya wasa saboda raunin da ya samu.

Federer ya fitar da Mischa da ci 6-1, 7-5, 6-2, inda zai shirya fafatawar gaba da Stan Wawrinka na Swiss.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.