Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan Kamaru za su yi da na sani- Doiuf

El Hadji Diouf.
El Hadji Diouf. (Photo : Reuters)

Tsohon dan wasan Senegal El Hadji Diouf ya ce, ‘yan wasan Kamaru guda takwas da suka ki amsa gayyatar kasar don buga mata gasar cin kofin Afrika a Gabon, za su yi da na sani har tsawon rayuwarsu. 

Talla

Diouf na cikin mutane na baya-bayan da suka fito fili suna bayyana takaici ko kuma mamaki kan yadda wasu zaratan ‘yan wasan Kamaru suka ki buga wa kasaru ta asali gasar.

Joel Matip na Liverpool da Eric Choupo-Moting na Schalke da kuma Allan Nyom na West Brom na cikin zaratan ‘yan wasan na Kamaru da suka yi watsi da gayyatar kasarsu.

Kamaru ce dai ta yi nasarar lashe kofin na Afrika bayan ta doke Masar da ci 2-1 a wasan karshe da suka fafata a Libreville.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.