Isa ga babban shafi
Wasanni-Najeriya

Tawagar Najeriya ta kwallon kafar rairayi ta tafi Bahamas

Tawagar kwallon kafar yashi ta Najeriya.
Tawagar kwallon kafar yashi ta Najeriya. sportloaded.com

Tawagar Najeriya ta kwallon kafar Yashi ko bakin teku, ta tashi zuwa birnin Bahamas na Amurka, inda zata fafata a gasar cin kofin kwallon kafar yashin ta duniya da za’a fara daga ranar 27 ga watan Afrilu zuwa 7 ga watan Mayu.

Talla

Kakakin hukumar kula da kwallon kafar Najeriya NFF Ademola Olajire ya ce ‘yan wasa 8 daga cikin 12 ne suka samu tafiyar karkashin mai horarwa Audu Adamu, yayinda sauran hudun zasu baya a ranar talata mai zuwa saboda jinkirin da aka samu wajen karba musu takardar Visa.

Yayin gasar kwallon yashin da ta gudana a shekara 2011 a kasar Italiya, Najeriya ta kammala gasar ce a matsayi na 7.

Najeriya na rukuni na biyu tare da Mexico, Italiya da kuma Iran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.