Isa ga babban shafi
wasanni

"Messi ya kere Roaldo na Real Madrid"

Lionel Messi na Barcelona
Lionel Messi na Barcelona Reuters/Albert Gea

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ce, har yanzu Lionel Messi ne gwarzon dan wasa a tarihi duk kuwa da irin nasarorin da abokin hamayyarsa na Real Madrid Christiano Ronaldo ke samu.

Talla

Jim kadan da lashe kyautar Ballon D’or da ake bai wa gwarzon dan kwallon shekara, Ronaldo ya bayyana kansa a matsayin dan wasa mafi shahara a tarihi, yayin da Barcelona ta bakin mai magana da yawunta Jopsep Vives ta yi watsi da ikirarinsa, in da ta ke ganin cewa, Messi ya kere shi.

A makon jiya ne dai Ronaldo ya lashe kyautar a karo na biyar, in da ya yi kan-kan-kan da Messi wajen lashe kyautyar.

A bangare guda, Barcelona ta magance rashin tabbas game da makomar Messi a kungiyar, in da ta tsawaita kwantiraginsa har nan da shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.